
Rahotanni sun bayyana cewa, akwai Gwamnoni ‘yan Jam’iyyar APC 7 dake munafurtar shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu.
Rahoton yace Gwamnonin suna turawa hadakar ‘yan Adawa kudade inda suke daukar nauyinsu a asirce dan kayar da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu zabe a shekarar 2027.
Jigo a jam’iyyar ADC na jihar Filato, Dr Sani Dawop ne ya gayawa kafar Punchng haka inda yace akwai rikici sosai a jam’iyyar APC.
Dama dai hutudole ya kawo muku cewa, akwai akwai gwamnoni 5 na jam’iyyar PDP dake shirin shiga jam’iyyar ADC amma sun ce a jira suga karshen rikicin jam’iyyar da Wike.