
Rahotanni sun bayyana cewa, tsaffin shuwagabannin Najeriya, Muhammadu Buhari da Abdulsalam Abubakar na can kwance a Asibitin kasar Ingila ba lafiya.
Rahotan yace rashin lafiyar tasu ta yi tsanani sosai, kamar yanda wata majiya ta bayyanawa kafar Sahara reporters.
Rahoton wanda yace wata majiya daga fadar shugaban kasa tace akwai yiyuwar tsaffin shuwagabannin kasar suna kan gargarar mutuwa ne.
Saidai ba’a bayyana wane irin ciwo ne ke damunsu ba.
Rahoton yace Abdulsalam Abubakar ya shafe watanni 5 a Asibitin yanzu.
Saidai shi bangaren tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari rahoton yace an kaishi cikin bangaren kulawa ta musamman an kuma sake kaishi ba sau daya ba.
A ranar Juma’a ne dai aka samu rahotan cewa, Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya kaiwa taaffin shuwagabannin kasar ziyara a Ingila inda ya duba lafiyarsu.
Duk da a hukumance ba’a bayyana irin rashin lafiyar dake damunsu ba amma majiyar tace Buhari na fama ne da ciwon hanci wanda ke cinsa a hankali, shi kuma Abdulsalam ciwon tsufa ne.