
Rahotanni daga birnin landan na kasar Ingila na cewa, tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya kwanta rashin lafiya.
Rahoton yace tsohon shugaban na can a bangaren kulawa ta musamman a wani asibitin kasar da ake kira da ICU.
Saidai rahoton yace tuni aka sallami tsohon shugaban kasar.
Kafar Empowered Newswire tace shugaban ya je landan ne dan kula da lafiyarsa inda a canne ya kwanta rashin lafiya.
Rahoton yace lamarin ya farune satin da ya gabata.
Ba dai a bayyana wace irin rashin lafiya ce ta kwantar da tsohon shugaban kasar ba amma rahoton yace yana can landan din yana kara samun sauki kuma da zarar ya warke zai dawo gida Najeriya.
Hakanan rahoton yace shima Mamman Daura yana can a landan din yana jinya.
A bikin cikar kungiyar ECOWAS shekaru 50 da aka yi ba’a ga tsohon shugaban kasar ba wanda rahotanni suka ce ya aikewa da shugaba Tinubu wasika inda yace ya je neman lafiya ne kasar waje shiyasa.