Friday, December 5
Shadow

Da Duminsa: Kasa da sati daya da saukar Ganduje daga shugaban APC, Gwamnan Kano, Abba Gida-Gida zai koma APC

Rahotannin da hutudole ke samu na cewa, Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf na shirin komawa jam’iyyar APC.

Hakan na zuwane kwanaki kadan bayan saukar Dr. Abdullahi Umar Ganduje daga mukamin shugaban jam’iyyar.

Mataimakin shugaban jam’iyyar APC reshen kudu maso gabas, Dr Ijeoma Arodiogbu ne ya bayyana hakan.

Yace wannan magana bawai jita-jita bace tabbas ce lokaci kawa ake jira nan da watanni 2 kowa zai shaida.

Dr Ijeoma Arodiogbu ya bayyana hakane a hirar da jaridar Punchng ta yi dashi inda yace sauran gwamnonin da zasu koma APC sune Gwamnonin jihohin Bayelsa, Rivers, da Plateau

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo: 'Yar majalisar Amurka, Nancy Mace ta nunawa abokan aikinta 'yan majalisa Bidiyonta tsirara wanda tace tsohon saurayinta ne ya dauke ta ba tare da izinin ta ba kuma tana son a hukuntashi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *