
Rahotanni sun bayyana cewa kasar Amurka ta Laftawa Najeriya sabon harajin kaso 15 cikin 100.
Hakan na zuwane bayan da kwanaki 90 da kasar ta Amurka ta ware dan tattaunawar huldar kasuwanci da Najeriya ta kusanto.
A watan Afrilu kasar Amurka ta kakabawa Najeriya harajin kasuwanci na kaso 14 cikin 100.
Saidai a wannan sabuwar sanarwar an sabunta tare da kara kaso 1 inda ya koma kaso 15 cikin 100.
Lamarin dai ba Najeriya kadai ya shafa ba hadda sauran kasashen Duniya da dama.