
Rahotanni sun bayyana cewa, kasar Amurka tace ta janye matakin soji da take son dauka akan Najeriya bisa zargin Kisan Kiristoci.
Tace a yanzu bayan ta fahimci yanda abin yake ta gane abune da za’a iya warwareshi ta hanyar diplomasiyya.
Amurkar ta canja matsayine bayan ganawar ‘yan majalisar kasar, Bill Huizenga da Reps. Michael Baumgartner, Keith Self, da Jefferson Shreve, babban me baiwa shugaban kasa shawara kan harkar tsaro Malam Nuhu Ribadu.
Tace ta fahimci akwai banbancin rikicin dake faruwa a Arewa maso gabas da Arewa maso tsakiya.
Tace amma zata ci gaba da aiki da Najeriya wajan ganin lamuran tsaro sun inganta.