
Rahotanni daga kasar Chadi na cewa, kasar ta kulle iyakokinta da Najeriya bayan bayyanar Rahoton cewa Amurka na iya kawo Hari Najeriya.
Kafar Zagazola Makama ce ta ruwaito cewa shugaban soji na kasar Chadi Muhammad Idris Derby Itno ne ya bayar da wannan sanarwar.
Yace sojojin kasarsa su tare iyakar kasar da Najeriya saboda ana tsammanin ‘yan Bindiga zasu iya tserewa can yayin da Amurka ke shirin kawo hari Najeriya.
Hakanan sanarwar tace kasar Chadi ba zata bari wasu ‘yan kasar waje su shigar mata kasa ba.