Majalisar zartaswa wadda ta hada da kungiyar gwamnonin Najeriya, NGF ta bayyana cewa tana baiwa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu shawarar ya dakata da maganar kara harajin VAT.
Kungiyar gwamnonin ta bakin gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde tace tana baiwa shugaban kasar shawarar ya dakata a wayarwa mutane da kai su fahimci abinda kudirin kara dokar VAT din ke nufi.
Sannan ya kamata a tuntubi masu ruwa da tsaki a kan harkokin al’umma dan jin shawarar su kan lamarin.
Ko da a baya dai, Kungiyar Gwamnonin Arewa da sarakunan yankin sun bayyana cewa basa tare da shugaban kasar kan karin harajin VAT.