Sunday, January 4
Shadow

Da Duminsa: Matatar Man Dangote ta dakatar da aiki

Rahotanni daga matatar man Dangote tace an dakatar da aiki a bangaren tace man fetur na matatar.

Hakan na zuwane daga bakin mataimakin shugaban kamfanonin Dangote me suna Devakumar Edwin wanda yace an dakatar da aikinne dan wasu ‘yan Gyare-Gyare.

Yace idan aka kammala gyaran yawan man fetur din da matatar ke tacewa zai karu daga ganga 650,000 kullun zuwa ganga 700,000 kullun.

Wannan dalili yasa tuni Depot dake sayarwa da ‘yan kasuwa man fetur suka kara farashin man su zuwa Naira 800 akan kowace lita.

Karanta Wannan  Talauci na karuwa a Najeriya, Musamman a kauyuka>>Inji Bankin Duniya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *