
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, ya fasa kai ziyarar da yayi niyyar yi zuwa jihar Ogun saboda abinda ya faru a jihar Filato.
Yace a yanzu zai kai ziyara jihar Filato ne dan jajantawa iyalan wadanda rikicin ya rutsa dasu sannan ya basu tabbacin samar da tsaro.
Yace daga can zai wuce Legas dan yin hutun good Friday sannan kuma zai yi ziyarar aiki a Lagos din da Ogun da Bayelsa.