Thursday, December 18
Shadow

Da Duminsa: Najeriya ka iya fadawa Duhu kwanannan saboda karancin gas da kamfanonin samar da wutar lantarki ke samu

Rahotanni sun bayyana cewa kamfanonin dake samar da wutar lantarki na Najeriya na fama da karancin gas wanda ake amfani dashi wajan samar da wutar.

Dalilin haka kuwa Najeriya na iya fadawa cikin duhu a yi bukukuwan kirsimeti babu wutar lantarki.

Kamfanonin rarraba wutar na Enugu da Fatakwal sun sanar da abokan hukdarsu cewa sun rage yawar wutar da suka baiwa mutane saboda wannan matsala.

Wata majiya ta tabbatarwa da Jaridar Punchng da wannan labarin.

Hakan na faruwa ne saboda gazawar gwamnati waja biyan bashin da kamfanonin iskar gas din ke bi wanda rahoton yace idan ba’a biya ba ka iya sa kasar ta fada Duhu.

Karanta Wannan  Ko Gezau: Barzanar Trump bata tsorata mu ba>>Inji Fadar Shugaban kasa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *