
A yayin rahoto yayi nisa cewa dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar Labour party a shekarar 2023, Peter Obi ya yadda yawa Atiku Abubakar mataimakin shugaban kasa a zaben shekarar 2027, Peter Obi din yayi martani kan wannan rahoton.
Peter obi dai bai karyata wannan rahoto ba amma yace Koma me za’a fada aje ai ta fada amma shi yayi hadaka dan kawar da matsalar rashin tsaro da yunwa a Najeriya.
Ya bayyana hakane a Kubawa Abuja wajan wani taro inda ya bayar da tallafi ga wata Makaranta.
Dama dai a shekarar 2019, Peter Obi da Atiku ne suka tsaya takarar shugabancin Najeriya amma tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya kadasu.