
‘Yan kwankwasiyya Bangaren Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf sun fito da sabuwar Hula me nuna cewa suna tare da Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu.
An ga Jar Hular me dauke da Tambarin Tinubu a jiki tana yawo a kafafen sada zumunta.

Hakan na zuwane yayin da Rahotanni suka ce ranar Litinin Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf zai koma jam’iyyar APC.