
Labarai da duminsu daga Abuja na cewa, sanata me wakiltar Abujan, Ireti Kingibe ta bar jam’iyyar Labour Party zuwa ADC.
Da take magana da manema labarai jim kadan bayan wani taro, Sanata Kingibe tace yanzu ita ta bar Labour Party zata koma jam’iyyar hadakar ‘yan Adawa ta ADC.
Tace zuwa yanzu bata karbi katin shiga jam’iyyar ADC ba amma maganar gaskiya ita ‘yar Jam’iyyar ce.