Friday, December 5
Shadow

Da Duminsa: Sanata Natasha Akpoti ta shirya da Sanata Godswill Akpabio har ma ta gayyaceshi…

Rahotanni daga majalisar dattijai na cewa akwai alamu masu karfi dake nuni da cewa, an shirya tsakanin Sanata Natasha Akpoti da Sanata Godswill Akpabio.

Hakan ya bayyana ne bayan da sanata Natasha Akpoti ta gayyaci Sanata Godswill Akpabio zuwa mazabarta Ihima, Kogi da kaddamar da wani aiki da ta yi.

Sanata Godswill Akpabio ne ya karanta takardar gayyatar a zauren majalisar Dattijai ranar Alhamis inda tace tana gayyatarshi da sauran sanatocin zuwa kaddamar da aikin.

A baya dai Sanata Natasha Akpoti ta zargi Sanata Godswill Akpabio ta neman ta da lalata wanda lamarin ya jawo zazzafar Muhawara.

Karanta Wannan  Da Duminsa:Aljanu sun je Asibiti Duba Adam A. Zango bayan da yayi Hadari

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *