
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya amince da canjawa jami’ar UNIMAID dake Maiduguri suna zuwa sunan tsohon shugaban kasa, Marigayi, Muhammadu Buhari.
Shugaban ya bayyana hakane a yayin zaman majalisar zartaswa na yau wanda aka yi shi musamman dan yiwa tsohon shugaban kasar, Muhammadu Buhari addu’a.
Shugaba Tinubu yace daga yanzu za’a rika kiran jami’ar ta UNIMAID da sunan Muhammadu Buhari University.