Friday, December 5
Shadow

Da Duminsa: Shugaba Tinubu zai gana da kamfanonin wutar Lantarki dan magance matsalar bashin da kamfanonin wutar ke bi

Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu zai gana da kamfanonin wutar lantarki dan magance matsalar bashin da kamfanonin wutar ke bi.

Ana sa ran Shugaban zai gana da kamfanonin ne inda za’a biya wani sashe na bashin da suke bi sannan sauran bashin za’a biyashi a hankali nan da watanni 6.

Hakan na zuwane bayan ganawar kamfanonin wutar da ministan wuta, Adebayo Adelabu.

Me magana da yawun Ministan, Bolaji Tunji ne ya tabbatar wa da manema labarai hakan a wata sanarwa da ya fitar.

Kamfanonin wutar na fuskantar matsalar karancin kudi wanda kuma suke bin bashin Naira Tiriliyan 4.

Karanta Wannan  Naira Miliyan 70 Tsohon shugaban kasa, Obasanjo ya so baiwa kowannen mu a matsayin cin hanci dan mu barsa ya zarce a karo na 3>>Sanata yayi Tonon Silili

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *