
Shugaban hukumar NMDPRA, Farouk Ahmed ya yi martani kan zargin da Attajirin Najeriya, Aliko Dangote ya masa na cewa ya kashe dala Miliyan $7 wajan biyawa ‘ya’yansa kudin makaranta.
Yace 3 daga cikin ‘ya’yansa sun samu scholarship inda aka biya musu kaso me yawa na kudin karatunsu.
Sannan yace akwai kudaden da mahaifinsa wanda dan kasuwane ya tara dan ilmin ‘ya’ya da jikoki sannan ‘yan uwa na taimakawa hakanan shima yana taimakawa ‘ya’yan nasa.
Yace ta hakane ya samu ilmantar da ‘ya’yan nasa amma ba sata yayi ba.