
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya ɗage tafiyar da ya shirya yi a yau zuwa Afirka ta kudu da kuma Angola, a yayin da ya ke jiran sauraron rahoto game da sace ɗalibai da aka yi a Kebbi da harin da aka kai kan wani coci a Kwara.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yauwansa, Bayo Onanuga ya fitar, Shugaban ya umurci a aika ƙarin jam’ian tsaro karamar hukumar Ekiti da ke jihar Kwara inda lamarin ya faru kamar yadda gwamnan jihar ya buƙata, tare kuma da bai wa ƴansanda umurnin farauto ƴan bindigar da suka kai hari kan masu ibadar.
A yau Laraba ne shugaban ya tsara barin ƙasar domin halartar taron shugabannin ƙasashe ashirin masu ƙarfin tattalin arziƙi (G20) karo na ashirin da za a yi a Afirka ta Kudu, daga nan kuma zai ƙarasa Luanda da ke Angola domin halartar karo na bakwai na taron ƙungiyar Tarayyar Afirka da ta Tarayyar Turai.
Sanarwar ta kuma ce a yanzu Tinubu na zaman sauraron rahoto daga mataimakinsa Kashim Shettima, wanda ya kai ziyarar jaje zuwa Kebbi a madadinsa, da kuma rahotanni daga ƴan sanda da hukumar tsaro ta farin kaya DSS kan harin coci a Kwara.