
Rahotanni daga kafar Sahara reporters wanda tace ta samo ta wasu majiyoyi sun ce wasu sojoji sun yi yunkurin yiwa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu juyin Mulki.
Sojojin sun shirya juyin Mulkinne ranar 1 ga watan Oktoba ta hanyar harbe shugaban kasar da wasu manyan jami’an tsaronsa sannan su ayyana gwamnatin Soja.
Rahoton yace sojoji 16 yanzu haka suna hannu wadanda suka fara daga mukamin Kaftin zuwa Brigadier General bisa wannan zargi.
Sahara reporters tace hukumar sojin tace an kama sojojin ne bisa laifuka daban-daban da suka aikata amma ba haka bane gaskiyar lamarin.
Majiyar tace an ce sun aikata wasu laifukane kawai dan ba’a so maganar ta fita.