
Wasu ‘yan Jam’iyyar APC magoya bayan Tinubu da Shettima sun fito zanga-zangar neman shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya kori Ministan babban birnin tarayya, Abuja Nyesom Wike.
Sun bayyana hakan ga manema labarai a budaddiyar wasika.
Sun mikawa shugaban jam’iyyar APC, Prof. Nentawe Goshwe Yilwatda wasikar inda suka bukaci ya mikawa shugaba Tinubu.
Sun Zargi Wike da sukar jam’iyyar APC da yi mata zagon kasa.