
Rahotanni na cewa, ‘yan Najeriya zasu iya samun saukin farashin Albasa saboda za’a shigo da Albasar daga kasar Nijar.
Farashin Albasa ya tashi sosai a Najeriya inda aka rika sayar da babban buhunta akan Naira N26, 000 wanda a baya ake sayarwa akan Naira 18,000.
Hakanan karamin buhun Albasar an rika sayar dashi akan Naira N19, 000 wanda a baya ana sayar dashi ne akan Naira N19, 000.
Tashin farasin Albasar ya samo Asali ne daga matsalar tsaro da sauyin yanayi da sauransu.