
Rahotanni daga fadar shugaban Najeriya dake Abuja sun bayyana cewa an samu daukewar wutar lantarki.
Matsalar wutar lantarkin ta farune a wasu sassan na Abuja wanda har ta kai ga lamarin ya taba fadar shugaban kasar.
Hukumar wutar lantarki ta Abuja, (AEDC) ta tabbatar da hakan a shafinta na X inda ta baiwa masu hulda da ita hakuri da kuma tabbacin cewa injiniyoyinta na aiki tukuru dan shawo kan matsalar.
Karin guraren da matsalar wutar lantarkin suka shafa sun hada da Lugbe da Kubwa.