
Rahotanni daga jam’iyyar ADC sun zargi shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta shirya taruka a asirce dan samo hanyar da zasu kwace iko da jam’iyyar ADC.
Me magana da yawun ADC na riko, Mallam Bolaji Abdullahi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai inda yace an kira taron inda wasu na kusa da shugaban kasar na ciki.
Ya bayyana cewa wannan ba shine Dimokradiyya ba sannan shiri ne na mayar da Najeriya tsarin jam’iyya daya kadai.
Yayi kira ga shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da ya jawa yaran nasa kunne inda yace idan da tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan haka yawa ‘yan Adawa da APC bata kafu ba har ta samu shugabancin Najeriya.