
Karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle da a yanzu haka ke jihar Kebbi ya bayyana cewa bayanan sirri da suke samu sun tabbatar musu da cewa suna daf da inda daliban da aka sace suke.
Yace sun baza jami’an tsaro a duk wata hanya da za’a iya bi dan guduwa da daliban.
Sannan ya bayar da yakinin cewa nan ba da jimawa ba za’a kubutar da daliban.