
Attajirin Najeriya, Femi Otedola ya bayyana cewa a lokacin kasuwancinsa na habaka sosai, bankuna suna aika mata kyawawan ‘yan mata dan su ja hankalinsa ya mayar da ajiyar kudi acan.
Ya bayyana hakane a wani littafin tarihin rayuwarsa da yanda ya gudanar da kasuwanci da yake shirin wallafawa wanda jaridar TheCable tace ta samu gani.
Yace ya samu matsala bayan da ya saro man fetur daga kasashen wajan lokacin man yana a farashin Dala $140 amma aka samu tsaiko be karaso Najeriya ba sai da ya koma farashin dala $40.
Yace hakan ya jefashi cikin matsanancin bashi.
Hakanan yace karya darajar Naira ma ya kara jefashi cikin wahala sosai.
Yace a lokacin da bashin bankin ya mai yawa kuma sai bankin suka koma aika masa da jigba-jibgan mazaje masu fadin kirji dan su bashi tsoro ya biya.