
Shugaban hukumar EFCC dake yaki da rashawa da cin hanci a Najeriya, Olanipekun Olukoyede yace a shekarar 2019 mahaifiyarsa ta rasu.
Yace ana kwana daya za’a binneta ya je gida dan halartar jana’izarta.
Yace akwai gidansa da ya gina tun kamin ya fara aiki da EFCC kuma a wancan lokacin yana mukamin sakatarene a hukumar, yace yana zuwa gida sai ya tarar da shanu an kawo masa.
Yace sannan kuma ya tarar da me gadinsa ya bashi wani akwati cike da Check na banki.
Yace da ya shiga gida sai matarsa ta daga hannu sama tace sun godewa Allah, amma anan ya taka mata birki, yace nan suka zauna suka duba duka kudaden da aka aika masa wanda sun kai Naira Miliyan 500.
Yace wadanda suka aika masa da wadanna kudade manyan ma’aikata ne da ministoci a ma’aikatun da suke bincike.
Yace a shekarar 2020 an fara bincikensa, yace da ace an ga wadannan kudade a cikin bankinsa na ajiyar kudi da ba zai tsallake wannan bincike ba.