
Gwamnan jihar Naija, Umar Bago ya bayyana cewa, daga yanzu sai an tantance hudubar Juma’a kamin a yadda limami ya hau Mumbari ya gabatar da ita.
Gwamnan ya tabbatar da hakan ne a hirar da aka yi dashi a hidan Talabijin na TVC ranar Lahadi.
Yace ba zasu amince da a rika yada hudubar data zama zata cutar da mutane ko gwamnati ba.
Gwamnan ya kara da cewa, suna aiki da hukumomin tsaro dan tabbatar da faruwar hakan.