Shugaban rukunin kamfanin Dangote,Aliko Dangote ya bayyana dalilin da yasa man fetur dinsa ya zama fari ba kamar wanda aka saba gani ba.
Dangote ya bayyana hakane bayan ganawa da manema labarai.
Yace man matatar man fetur dinsa ya zama farine saboda zai fi zama me lafiya wanda ba zai cutar da muhalli ba ba kamar wanda aka saba gani ba.
Yace kuma man fetur dinsa zai zama wanda baya cutar da ababen hawan mutane ba kamar wanda aka Saba amfani dashi ba.