
Sanata Natasha Akpoti daga jihar Kogi ta bayyana kalaman batsa da Sanata Godswill Akpabio ya gaya mata bayan da ta je ofishinsa.
Tace ta je ofishinsa ne dan jin ba’asin abinda yasa ba’a amincewa da kudirorin dokar da take kawowa majalisar inda ta bayyana cewa, kudirorin na da matukar muhimmanci a wajan jama’ar mazabarta.
Tace tana mai magana kawai sai yace mata idan tana son kudirorin data kawo su wuce to sai ta yadda ta jiya masa dadi.
Tace sai ta yi kamar bata ji ahinda yace ba ta ci gaba da maganarta, tace amma ya sake gaya mata cewa, zabi ya rage nata.
Sanata Akpoti ta bayyana hakane a hirar da aka yi da ita a gidan talabijin na Arise TV inda ta zargi Sanata Akpabio da neman yin lalata da ita.