
Rahotanni sun bayyana cewa, dan shugaban kasa, Seyi Tinubu ya cika shekaru 40 da haihuwa.
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya taya dan nasa murna.
A wani mataki na nuna murna da wannan rana, An shirya raba Baibul har guda Miliyan daya a fadin Najeriya.
Hon. Belusochukwu Enwere ne ya bayyana haka a cibiyar kiristanci ta kasa dake Abuja ranar Lahadi.
An yiwa Seyi Tinubu addu’a a coci guda 40 a fadin Najeriya saboda murnar wannan rana.