
Aliko Dangote ya nemi shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da ya saka man fetur cikin abubuwan da aka haramta shigo dasu cikin Najeriya.
Saidai ‘yan kasuwar man fetur sun ce basu yadda da hakan ba.
Dama dai akwai dokar data hana shigo da kayan da ake iya yinsu a Najeriya daga kasashen waje, shine Dangote yake son a saka Man fetur a ciki.
Dangote yace ci gaba da shigo da gas da man fetur daga kasashen Turai zai sanyaya gwiwar matatun man fetur da ake dasu a Najeriya.
Yace bama Najeriya kadai ba hadda sauran kasashen Africa ya kamata a hana shigo da man fetur daga kasashen turai.