
Matatar man fetur ta Dangote ta bukaci ‘yan Najeriya dasu saka ido akan duk gidan man MRS dake sayar da man fetur sama da Naira 739 akan kowace lita su kai kararshi.
Sanarwar tace matatar man Dangote tuni ta fara sayar da man akan wannan farashin ta hanyar gidajen man MRS dake fadin kasarnan.
Sannan za’a samar da wadataccen man dan kaucewa wahalar man da ake yawan fuskanta kusan duk karshen shekara.
Sanarwar ta bayar da lambar wayar da za’a kira dan kai korafin kamar haka: 0800 123 5264