
Kungiyar ‘yan kasuwar man fetue ta kasa, IPMAN ta yi martani game da rage farashin man fetur din da matatar man fetur din Dangote ta yi jiya Alhamis.
Matatar man fetur din Dangote ta rage Naira 15 akan kowace lita kamar yanda ta sanar a jiya.
Saidai shugaban kungiyar ‘yan kasuwar, Chinedu Ukadike yace su lamarin ya zama riba da asara a wajansu, yace yanzu wadanda suka sayi man fetur din a wajan Dangote a tsohon farashi in ba sa’a ba zasu tafka Asara ne.
Sannan kuma su ‘yan kasuwa dake shigo da man fetur din suma saidai su je su samu man fetur din dake da Arha su siyo.
Yace Dangote na amfani da rage farashi ne da ya zama shi ne ke da wuka da nama akan samarwa da raba man fetur a kasarnan.