
Rahotanni sun bayyana kan dalilin da yasa Dangote ya kori ma’ikatan Najeriya 800 daga aiki sannan dalilin da yasa ya ki mayar dasu aiki.
Dangote yace ya samesu da yi masa zagon kasa ne wanda hakan ya shafi yanayin matatar.
Saidai korar ma’aikatan ya tilasta kungiyar manyan ma’aikatan man fetur da Gas, PENGASSAN shiga yajin aiki dan Dangoten ya mayar da wadancan ma’ikata da ya sallama daga aiki.
Saidai Dangote yace shi fa ba zai mayar da ma’ikatan da bai yadda dasu ba bakin aiki, dalili kuwa shine zasu yi masa zagon kasa.
Dangote yace zai biya ma’aikatan albashi har na tsawon shakeru biyu ba tare da suna zuwa aiki ba, saidai Gwamnatin tarayya ta ja hankalinsa kan yawan kudin da zai kashe idan yace zai yi hakan.
Amma Dangote yace ya amince yayi asarar biyansu kudin Albashi ba tare da suna zuwa aiki ba maimakon ya mayar dasu aiki su lalata masa matatar mansa.
Saidai Kungiyar PENGASSAN bata amince da wannan tayi na Dangote ba.
A karshe dai Dangote ya yadda ya mayar da ma’aikatan bakin aiki amma ba a matatar ta Dangote ba, zai rabasu ne zuwa sauran kamfanoninsa.