
Matatar Man fetur ta Dangote ta rage farashin Man Fetur.
A yanzu farashin yana akan Naira ₦760 ne kan kowane kilo maimakon Naira ₦810 da ake saye a baya.
Sauran masu samar da gas din girki a Najeriya irin su Matrix da Ardova suna sayar da gas dinne akan farashin Naira ₦920
Su kuwa AY Shafa da NIPCO suna sayar da gas dinne akan farashin Naira ₦910.
Su kuwa Stockgap Depot suna sayar da gas dinne a farashi Naira ₦950 kan kowacce Lita.
Hakan ya bayyana cewa, Gas din Dangote shine mafi Arha a Najeriya.
Ana ganin hakan zai iya tilasta sauran masu samar da gas a Najeriya suma su rage farashinsu.