
Dansandan Najeriya me suna Maxwell Zabu ya Harbi Kansa inda ya mutu har Lahira.
Dansandan na aikin baiwa tsohon shugaban karamar hukumar Fatakwal ta jihar Rivers, Victor Ihunwo kariyane inda a ranar Talata ta harbi kansa ya mutu.

Lamarin ya farune a Eagle Island gidan tsohon shugaban karamar hukumar.
Kakakin ‘yansandan jihar, Grace Iringe-Koko ta tabbatar da faruwar lamarin inda tace suna kan bincike.