Farashin Naira ya fadi a kasuwar canji ta bayan fage data gwamnati.
A kasuwar Gwamnati an sayi dalar akan Naira N1689.88 ranar Litinin inda a ranar Talata kuma aka sayi Dalar akan N1681.42.
Inda a kasuwar bayan fage kuwa an sayi dalar akan Naira N1735 ranar Litinin amma ranar Talata aka sayeta akan Naira N1740.
Hauhawar farashin dala dai na daya cikin abubuwan dake sanya kayan masarufi na tsada a Najeriya.