
Rahotanni daga babban bankin Najeriya, CBN yace darajar Naira ta karu inda aka sayi dalar Amurka akan Naira 1,497.5
Hakan ya fito ne daga babban bankin Najeriya, CBN inda kuma aka samu kudin ajiyar Najeriya a kasashen waje na dala ke kara hauhawa.
Masana tattalin arziki sun ce hakan alamace ta cewa tattalin arzikin Najeriya na kara hauhawa.
Wannan shine karo na farko da Naira ta je kasa da 1,500 akan kowace dala daya tun farkon shekarar 2025.