Monday, March 24
Shadow

Dattawan arewa sun buƙaci Tinubu ya mayar da Fubara bakin aiki

Ƙungiyar dattawan arewa ta nuna rashin jin daɗinta kan dakatar da gwamnan jihar Rivers da majalisar dokokin jihar da Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya yi.

A wata sanarwa da kakakin ƙungiyar Farfesa Abubakar Jika ya fitar, ya yi kira ga Tinubu da ya yi gaggawar mayar da gwamnan da mataimakinsa bakin aikinsu.

Ƙungiyar ta ce duk da cewa sashe na 305 ya ba shugaban ƙasa damar ayyana dokar ta-ɓaci, “babu hujjar da za ta sa a ayyana dokar a jihar Rivers a yanzu,” kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

“Dole ne shugaban ƙasa ya lalubo hanyoyin da za a warware matsalar rikicin siyasar jihar Rivers ɗin, sannan ya dakatar da dakatarwar da ya yi gwamnan da mataimakinsa da majalisar dokokin jihar domin tabbatar da wanzumar dimokuraɗiyya da adalci.”

Karanta Wannan  Sabon mai baiwa Gwamnan Kano shawara ya rasu kwana ɗaya da rantsar da shi

Haka kuma ƙungiyar ta yi gargaɗi ga Tinubu da ya sa ido sosai domin tabbatar da ganin rikice-rikicen da ake fama da su a wasu jihohi, “irin Kano da ke fama da matsalar rikicin masarauta ba su rincaɓe ba.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *