Ƙungiyar dattawan Arewacin Najeriya ta koka kan rashin shigar da ƙwararu a kwamitin da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya umarci ofishin ministan shari’a da na majalisar ƙasar su kafa domin sake duba ƙudurorin cikin tsanaki.
Ƙungiyar ta ce bai kamata gwamanti ta nemi a kawo sauye-sauye cikin gaggawa kan batun dokar harajin ba, inda ta ce aiwatar da dokar ba tare da tuntuɓa yadda ya kamata ba zai yi wa jihohin yankin illa.
Farfesa Abubakar Jika Jiddere ɗaya ne daga cikin shugabanin ƙungiyar ya ce kawo yanzu sun kamala yi wa dokar harajin duba na tsanaki kuma sun haɗa rahotonsu, wanda haka yasa suke ganin dole a sake nazari kan ƙudurin.