Friday, December 5
Shadow

David Mark zai shagabanci jam’iyyar ADC ta hadakar ‘yan adawa

Rahotanni sun bayyana cewa, tsohon kakakin Majalisar Dattijai, Sanata David Mark ne ake sa ran zai jagoranci Jam’iyyar hadaka ta ‘yan Adawa watau ADC.

Ana tsammanin nan gaba kadanne hadakar ‘yan adawar zasu bayyana ADC a matsayin jam’iyyar da zasu yi amfani da ita wajan kalubalantar shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a zaben shekarar 2027 kuma David Mark ne zai zama shugaban jam’iyyar na rikon kwarya.

Rahoton yace hadakar ‘yan adawar ta hada da Atiku Abubakar, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai, Rotimi Amaechi, da Peter Obi.

Jaridar Punchng tace David Mark ya amince ya zama shugaba jam’iyyar ta ADC.

Rahoton yace hadakar ‘yan adawar na neman wanda zai zama sakataren jam’iyyar tasu bayan da Rauf Aregbesola, da Senator Ben Obi suka ki amincewa da tayin zama sakataren jam’iyyar.

Karanta Wannan  Labari me Dadi: Za'a sake rage farashin man fetur

Ana tsammanin cikin satin da zamu shiga ne ‘yan adawar zasu fitar da cikakkiyar sanarwa kan lamarin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *