Aƙalla mutum 10 ne suka mutu a birnin New Orleans da ke Amurka lokacin da wata mota ta kutsa cikin dandazon mutane da asubahin ranar farko ta sabuwar shekara.
Aƙalla mutum 35 ne suka samu rauni a lamarin.
Ƴansanda sun ce wani mutum ne ya tuƙa wata motar a-kori-kura a guje cikin dandazon mutane a guje, da niyyar kaɗe mutane da dama.
Haka nan direban motar ya buɗe wuta kan ƴansanda bayan motar tasa ta tsaya, lamarin da ya sa ya raunata jami’ai biyu.
Wani jami’in Hukumar bincike ta FBI ya ce an kuma samu wani abu da ake zaton abin fashewa ne a wurin da lamarin ya faru, sai dai ya ce ba hari ba ne na ta’addanci – duk kuwa da cewa magajin garin birnin ya yi zargin hakan.
An gargadi mutane su ƙaurace wa wurin da lamarin ya faru.