Friday, March 21
Shadow

Dokar ta-ɓaci a Rivers cin zarafin dimokraɗiyya ne – Atiku

Ɗantakarar shugaban Najeriya ƙarƙashin jam’iyyar PDP a babban zaɓen ƙasar na 2023, Atiku Abubakar ya bayyana matakin da shugaba Bola Tinubu ya ɗauka a jihar Rivers a amatsayin nuna iko a siyasa.

Ya bayyana cewa ga masu bibiyar yadda rikicin Rivers ke kasancewa sun san cewa Bola Tinubu ya kasance mai ruwa da tsaki a rikicin siyasar da ya mamaye Rivers.

“Kau da kai da kuma nuna ko oho wajen kare ta’azzarar rikicin abin kunya ne.” kamar yadda Atiku ya bayyana.

Ya ce abu ne da ba za a yafe ba, yadda aka ƙara jefa yankin Neja Delta cikin rikici da rashin kwanciyar hankali – lamarin da ya warware ƙoƙarin samar da zaman lafiyar da tsohon shugaban Najeriya, Umaru Musa Yar’adua ya yi.

Karanta Wannan  Dukkan alamu sun nuna Jam'iyyar mu ta kama hanyar rugujewa>>PDP

“An wanke shekarun da aka shafe da samun cigaba saboda kawai wata buƙata ta ƙashin kai.” in ji Atiku.

A cewarsa, matakin na Tinubu ci zarafin dimokraɗiyya ne kuma ya zama dole a yi kakkausar suka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *