
Babban Lauyan Najeriya, Femi Falana, SAN ya bayyana cewa, dokar tilastawa ‘yan Najeriya sai sun yi zabe ba zata yi aiki ba.
Majalisar wakilai ta fara tattaunawa akan wani kudirin doka da kakakin majalisar, Tajuddeen Abbas ya gabatar da ya bukaci kowace dan Najeriya me hankali dole ya rika yin zabe.
Dokar dai har ta tsallake karatu na 2.
Saidai a nasa jawabin, Femi Falana yace wannan doka ba zata yi aiki ba.
Yace dokar Najeriya ta tanadi a baiwa dan Najeriya damar ya yi tunani akan wanda zai zaba sannan doka ta bashi damar ya boye wanda ya kadawa kuri’ar.
Yace dan haka wannan doka ba zata yi aiki ba duk da yasan cewa ana kokarin zartas da itane dan karfafawa mutane yin zabe.