
Babban malamin addinin Islama, Sheikh Dr. Ahmad Gumi ya bukaci Gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta nemi shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya janye barazanar da yawa Najeriya.
Yace shugaba Tinubu ya kira jakadan Amurka ya bukaci kasardu ta janye barazanar da tawa Najeriya.
Sheikh Gumi yace kasa bata fi kasa ba, Najeriya kasa ce me con gashin kanta dan haka bai kamata ta tsaya ana gaya mata abubuwan da basu kamata ba.
Sheikh Gumi yace idan Trump yaki janye kalaman nasa, Najeriya ta yanke huldar jakadancin da Amurkar.
Ya kuma baiwa Gwamnatin shawarar cewa, ta fara neman wasu abokan huldar kasuwanci da sayen makamai bayan Amirka.