
Malamin addinin Islama, Dr. Ahmad Gumi ya maka wasu mutane 2 a kotu saboda zargin bata masa suna.
Malam ya shigar da karanne ta hannun lauyansa, Suleiman Danlami Lere, Esq., kuma wadanda ake Tuhuna sune George Udom da- Bello Isiaka.
Ana zarginsu da yada wani rubutu da suka dangantashi da Sheikh Gumi inda suka ce wai yawa sabon Ministan tsaron, Christopher Musa barazanar cewa wai idan bai daina kaiwa Tshàgyèràn Dhàjì hare-hare ba, zai kaiwa iyalansa hari.
Sheikh Gumi yace wannan rubutu karyane kuma bashi yayi shi ba.