
Hukumar ‘yansandan Najeriya reshen jihar Rivers sun gargadi ‘yan mata dake karbar kudin mota a hannub samari da niyyar cewa zasu je a hadu amma su ki zuwa.
Hukumar tace hakan laifi ne na zamba cikin aminci da kuma samun kudi ta hanyar karya, hukumar tace idan saurayi ya shigar da kara, za’a iya hukunta budurwar.
Kakakin ‘yansandan jihar, Grace Iringe-Koko ce ta bayyana hakan a shafinta na X inda ta jawo hankalin mutane su daina neman kudi ta hanyar da bata dace ba.