
Gwamnatin tarayya ta saba alkawarin data wa matasa masu bautar kasa, NYSC fara biyansu Alawus din Naira 77,000 a watan Fabrairu inda har yanzu ta ci gaba da biyansu Naira 33,000.
Da yawan matasa masu bautar kasa da suka karbi alawus din nasu a daren ranar Juma’a sun bayyana ganin Naira 33,000 maimakon Naira 77,000 da aka musu Alkawari.
Hakan ya sabawa maganar da shugaban hukumar ta NYSC, Brigadier General Yushau Ahmed yayi a watan Janairu da ya gabata inda yace maganar karin kudin tabbatacciya ce kawai ana jiran akincewa da kasafin kudin shekarar 2025 ne.
Zuwa yanzu dai babu wani karin bayani kan lamarin daga gwamnati wanda hakan ya bar matasan cikin damuwa.
Lura da yanda matsin tattalin arziki yayi yawa, Naira 33,000 babu inda zata kai matasan masu bautar kasa.