Tun a shekarar 2019 ne gwamatin tarayya ta kashe Biliyoyin Naira dan samar da tsaro a iyakokin Najeriya musamman dan hana baki daga kasashen Chad, Niger, Mali, Cameroon, da Benin Republic shigowa Najeriya.
Mutanen dake shigowa daga wadannan kasashe ne ake zargi da hannu a matsalolin ta’addanci da garkuwa da mutane da sauransu.
Hakanan a wannan Gwamnati ta Bola Ahmad Tinubu, Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo ma ya bayyana cewa, a yanzu haka ana kan saka kyamarori da sauran kayan aiki na zamani a iyakokin Najeriya dan hana baki da basu da takardun izini shigowa Najeriya.
Yace a yanzu haka, fiye da rabin iyakokin Najeriya an saka musu kyamarorin inda yace kuma aiki na kan ci gaba.
Hakanan yace akwai jami’an hukumar kula da shige da fici ta Immigration dake kula da yanda wadannan kyamarori ke aiki.
Saidai Binciken jaridar Punchng ya ruwaito cewa, har yanzu bakin da basu da takardun da suka kamata suna shigowa cikin kasarnan ba tare da matsala ba.